Arsenal ta sayi Yaya Sanogo

Yaya Sanogo
Image caption Yaya Sanogo

Kulob din kwallon kafa na Arsenal ya sayi dan wasan nan mai shekaru 20 dan kasar Faransa, Yaya Sanogo daga kulob din Auxerre.

Sanogo ya fara wasa a kulob din dake cikin gasar Premier ne, bayan kwantiraginsa ya kare da Ligue 1.

Dan wasan wanda ya zura kwallaye 11 a wasanni 24 da ya yiwa Auxerre, na tare da kungiyar Faransa a halin yanzu, inda yake buga wasa a gasar cin kofin kwallon duniya na 'yan kasa da shekaru 20 a Turkiyya.

Kuma ya ci kwallaye biyu a wasan rukuni-rukuni, abin da ya taimaka wa kungiyarsa ta kasance cikin kungiyoyin kwallon kafa 16 dake wasan, kuma za su fafata da mai masaukin baki.

Shugaban Arsenal, Arsene Wenger yace " Sanago matashi ne da muka yi dacen sayensa."

Ya kara da cewa "Ya nuna cewa yana da hazaka, idan ka dubi rawar da ya taka a Auxerre da kuma ga kungiyar 'yan kasa da shekaru 20 ta Faransa."

Sai dai kulob din bai bayyana ko a kan kudi nawa ya sayi dan wasan ba.