Koci Saintfeit zai taimakawa Malawi

Image caption Tom Saintfeit zai taimakawa Malawi

Kasar Malawi ta baiwa Tom Saintfeit aiki a fagen masu bada horo na kulob din inda suka cimma yarjejeniyar kwantaragin watanni biyu.

Saintfeit ya ce aikin da zai yi shi ne taimakawa Malawi ta sami fitowa Gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa da za a yi a Brazil a shekara ta 2014.

Malawi za ta buga wasanta na karshe na rukunin F da Najeriya ranar 6 ga watan Satumba- idan suka ci za su sa ran fitowa gasar.

Kociyan mai shekaru 40, wanda ya yi Kociyan Namibia, da Zimbabwe da Habasha zai ba da horon ne ga Malawi kyauta.

Karin bayani