Steve McClaren ya koma QPR

Image caption Steve McClaren ya koma QPR

Tsohon manajan Ingila Steve McClaren ya koma Queens Park Rangers a matsayin Koci a karkashin shugabancin Harry Redknapp.

Kocin mai shekaru 52, ba shi da aiki tun lokacin da ya bar Kulob din FC Twente a watan Fabrairu.

Rednapp dai ya ce yana son sababbin dabaru, da ra'ayoyi daban daban da kuma jagora gogagge.

Yanzu dai Redknapp ya karawa ma'aikatan ba da horo karfi saboda kara McClaren da ya yi.

Karin bayani