Kulob din Swansea ya sayi Shelvey

Jonjo Shelvey
Image caption Jonjo Shelvey ya koma Swansea

Kulob din Swansea City ya kammala yarjejeniyar daukar dan wasan tsakiyar nan Jonjo Shelvey akan kudi fam miliyan biyar daga kulob din Liverpool.

Dan wasan mai shekaru ashirin da daya a duniya dai ya sanya hannun yarjejeniyar shekaru hudu kwarara tare da kulab din na South Wales.

Sai dai ance kulab din Crystal Palace ma yaso ya dauki dan wasan

Shelvey, dai yanzu ya zama dan wasa na dindindin da Kulob din na Swansea ya dauka na shida, cikin wadanda suka sanya hannu a kakar wasannin.

Karin bayani