Taye Taiwo ya koma Bursaspor

Taye Taiwo
Image caption Taye Taiwo ya bar AC Milan

Dan wasan Najeriyar nan mai tsaron baya Taye Taiwo ya kamala komawarsa zuwa bangaren Turkiyya na Bursaspor daga Kulob din AC Milan

Taiwo wanda ya bugawa Kulob din Ukrain na Dynamo Kiev wasa a matsayin aro a kakar wasannin data gabata, ya haye gwajin lafiyar da akai masa kafin ya kammala sanya hannun kwanturagin shekaru uku da Kulob din a ranar asabar.

Dan wasan mai shekaru 28 a duniya ya hade da Milan daga Marseille a lokacin bazarar shekarar 2011.

Ya kuma fadawa BBC cewa yayi murnar komawa Kulob din na Bursaspor.