Everton ta dauki Arouna Kone

Arouna Kone
Image caption Arouna Kone ya koma Everton

Kulob din Everton ya dauki dan wasan gaban Wigan Arouna Kone a wata yarjejeniyar shekaru uku akan kudaden da ba ba bayyana su ba.

Kulob din Newcastle da Everton duka sun nemi sayen dan wasan mai shekaru ashirin da tara a duniya.

Amma dan wasan haifaffan kasar Ivorycoast ya zabi tafiya Everton inda zai sake haduwa da Roberto Martinez wanda ya bar Kulob din Wigan a karshen kakar wasanni.

Kone dai ya zurwa gola golai goma sha daya a wasan Primiya Lig a kakar wasannin data gabata.

Karin bayani