Ghana ta kai zagayen kusa da karshe

Wasu 'yan wasan kasar Ghana
Image caption Wasu 'yan wasan kasar Ghana

Kungiyar kwallon kafa ta Ghana ta shiga cikin kungiyoyi hudun da suka rage, a gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru ashirin da ake yi a Turkiyya.

Hakan ya biyo bayan lallasa kungiyar kasar Chile da Ghanan ta yi, a karawar da suka yi a zagayen gab da na kusa da na karshe.

Ghana ta zura kwallaye hudu a ragar abokiyar karawarta, yayin da Chile ta farke uku daga cikinsu.

An kammala mintoci 90 na wasan ne kowannesu na da ci bi-biyu, amma a karin lokacin da aka yi Ghana ta doke Chile.

A zagayen na kusa da na karshen dai Ghana za ta kece raini ne da Faransa, yayin da ita kuma Iraqi za ta gwabza da Uruguay.

Kocin Ghana Sellas Tetteh ya nuna farin ciki da kungiyar ta kawo wannan mataki.