Liverpool ta ki sayar da Suarez

Luis Suarez
Image caption Liverpool ta yi watsi da tayin sayen Suarez

Kulob din Liverpool yaki amincewa da tayin sayen dan wasan gabansa Luis Suarez a kan kudi Fam miliyan talatin daga Kulob din Arsenal.

Kulob din Liverpool dai yaki cewa uffan akan rahotannin tafiyar dan wasan gaban zuwa Kulob din Arsenal, kuma a baya ma Liverpool sun hakkake cewa Suarez bana sayarwa bane.

Sai dai an fahimci cewa an yi tayin sayen sa, amma sukai watsi da tayin.

Shima dai dan wasan har yanzu ance bai nuna Kulob din da yake son ya koma ba tukuna.

A yanzu haka dai Suarez yana hutu bayan ya yiwa Uruguay wasa a gasar cin kofin nahiyoyi a Brazil, kuma ba a tsara zai koma Kulob dinsa ba har sai karshen wata, wanda daga nan ne kuma za a san ina ne makomarsa.

Karin bayani