Benteke ya mika bukatar barin Villa

Christian Benteke
Image caption Benteke shi ne dan wasa na hudu da ya kowa zura kwallaye a gasar premier ta shekarar 2012-13

Dan wasan gaba na kulob din Aston Villa, Christian Benteke ya mika wa kulob din bukatarsa ta komawa wani kulob din, ko da yake Villa na son ya zauna.

Dan wasan mai shekaru 22 wanda aka sayo daga Genk a kan fam miliyan bakwai a bara, ya zura kwallaye 23 a duka wasannin da Villa ta buga.

Villa ta shaida wa Benteke, wanda ake cewa Arsenel da Chelsea da Tottenham na sha'awar sayensa cewa, kulob din zai duba tayin da ya dace.

"Idan kuma ba haka ba, to zai ci gabada buga wa Villa wasa" a cewar wata sanarwar da kulob din ya fitar.

"An tuna masa cewa akwai sauran shekaru uku a kwantiraginsa, saboda haka mun dauke shi dan wasan Villa, kuma muna sa ran zai kasance tare da mu a kakar wasannin shekarar 2013 zuwa 2014."

Benteke bai bi tawagar kulob din zuwa Jamus ba domin buga wasannin share fagen kakar wasanni, amma Villa ta ce da ma can ta bashi hutu har zuwa 18 ga watan Yuli, kafinma ya mika bukatar neman koma wa wani kulob din.

Manajan kulob din Paul Lambert yace bai ji dadi ba matuka da neman barin kulob din da dan kasar Belgium din ya yi.