An dakatar da kungiyoyin wasanni a Najeriya

Image caption NFF ta ce za ta gudanar da binciken kwa-kwaf game da batun

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta dakatar da kungiyoyi hudu na kwallon kafar kasar saboda sun ci kwallayen da suka wuce kima.

Kungiyar Plateau United Feeders ta doke Akurba da ci 79 ba ko daya, yayin da kungiyar Police Machine ta lallasa Bubayaro da ci 67 ba ko daya a wasannin raba-gardamar da suka buga.

A cewar shugaban kwamatin tsare-tsare na NFF, Mike Umeh, '' Ba za mu yarda da irin wannan magudi wanda ya wuce-gona-da-iri ba. Don haka mun ladabtarwa da kungiyoyin sai baba-ta-gani. Za mu yi nazari kan matakin horarwa na gaba da za mu dauka''.

Hukumar ta kara da cewa za ta gudanar da cikakken bincike game da wannan batu, tana mai cewa za ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo a kan duk wanda ta samu da hannu a cikin wannan badakala.

Karin bayani