Gebresellasie zai shiga siyasa

Image caption Gebrselassie ya ce yana son taimakawa don ci gaban kasarsa

Shahararren dan tseren nan dan kasar Ethiopia, Haile Gebresellasie, ya tabbatar da labarin da ke cewa zai shiga fagen siyasa da zarar ya ajiye takalminsa na tsere.

Dan tseren, wanda sau biyu yana lashe wasan tseren mita dubu goma a Gasar Olympic, ya bayyana a shafinsa na Tweeter cewa yana son zama dan majalisar dokokin kasar a shekarar 2015, domin ya taimaka wajen ci gaban kasar.

Har yanzu dai Gebresellasie yana ganiyar sa a tsere, domin kuwa koda a watanni ukun da suka gabata ya lashe gasar tseren yada-kanen-wani ta Vienna .

Karin bayani