Pellegrini zai sauya salon wasa a City

Image caption Pellegrini bai bayyana hanyar da zai bi domin sauya salon wasa a Manchester City ba

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce daya daga cikin dalilan da suka sanya aka nada shi shi ne domin ya tabbatar 'yan wasa suna yin wasa mai kayatarwa.

Kocin dan kasar Chile, mai shekaru 59 a duniya, ya maye gurbin Roberto Mancini bayan ya bar Malaga.

A hirarsa ta farko da manema labarai tun da ya koma City a watan Yuni, Pellegrini ya ce: "Magoya bayan Man City za su ga sauyi game da yadda ake buga wasa a kungiyar, sabanin yadda ake yi a shekarun baya. Za mu yi kokarin ganin an rika yin wasanni masu armashi''.

An kori Mancini daga kungiyar ranar 13 ga watan Mayu, ana dab da cika shekara guda bayan kungiyar ta lashe Gasar Premier.

Duk da cewa ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofin Premier da na FA Cup a shekaru uku da ya yi yana shugabanicin kungiyar, amma an yi ta sukarsa saboda salon kare gida da yake amfani da shi lokacin wasa.

Pellegrini, wanda ake yi wa lakabi 'injiniya' saboda ya karanta fannin Injiniya, bai yi cikakken bayani kan yadda zai sauya fasalin kungiyar ba.

Karin bayani