Pep Guardiola na son sayen Alcantara

Image caption Guardiola ya ce Alcantara dan wasa ne gagara-misali

Kocin Bayern Munich, Pep Guardiola, yana son sayen dan wasan tsakiya na Barcelona, Thiago Alcantara, wanda rahotanni ke cewa Manchester United ma na son sayensa.

Guardiola ne ya bai wa dan wasan, dan kasar Spain mai shekaru 22 a duniya damar fara shiga manyan kungiyoyin kwallon kafa, lokacin da ya dauke shi a watan Mayu na shekarar 2009, yayin da yake da shekaru 18.

A cewar Guardiola: "Indai ba Thiago muka saya ba, ban san abin da zai faru ba. Za mu jira tukuna mu ga abin da zai faru.Na san shi sosai a matsayin dan wasa kwararre, gagara-misali."

Guardiola ya kara da cewa Thiago dan wasa ne da ke iya buga wasa a matsayi uku, ko hudu ko biyar.

Kocin ya ce yana fatan Thiago zai koma Bayern Munich domin ya samu karin dama ta zuwa Gasar cin kofin duniya a badi.

Karin bayani