Ci gaban Ingila ne Burina: Dyke

Greg Dyke
Image caption Greg Dyke na bukatar ganin an samu karin matasan Ingila a Premier

Sabon shugaban Hukumar kwallon kafa ta Ingila Greg Dyke, ya ce daya daga cikin abubuwan da zai sa a gaba shi ne ci gaban kungiyoyin kasa na Ingila.

Sabon shugaban mai shekaru 66 ya kama aiki ne a wannan matsayi ranar Asabar inda ya maye gurbin David Bernstein.

Rabon da kungiyar 'yan wasan Ingila manya ta kai wasan kusa da na karshe a wata babbar gasa tun 1996.

Sabon shugaban ya ce, ''rabon da Ingila ta samu wata nasara ta a-zo-a-gani tun wannan shekara, kuma ina ganin daya daga cikin kalubalen ci gaban shi ne ta yaya za mu samu kyakkyawar kungiyar 'yan wasa ta Ingila.''

Babbar kungiyar 'yan wasan kasar ta Ingila ta yo kasa a jerin gwanayen kasashe na duniya na FIFA zuwa matsayi na 15.

Matakin da kungiyar ba ta taba fadowa ba a shekaru biyar.

Su kuwa kungiyoyin kwallon kafar kasar na 'yan kasa da shekaru 21 da 20 da kuma 19 sun samu nasarar wasa daya ne daga cikin tara.

Wani bincike ya nuna cewa 'yan wasan Ingila 'yan kasa da shekara 21, 35 ne kawai suka yi wasan Premier a bara.

Kuma wannan shi ne mafi karanci tun shekara ta 2005.

Saboda haka sabon shugaban na FA ya ke ganin wannan abu ne da za a yi gyara a kai.

Karin bayani