Gay da Powell sun yi amfani da kwayoyi

tyson gay da asafa powell
Image caption Gay da Powell dukkanninsu sun ce ba su yi amfani da kwayoyin kara kuzari da niyya ba

An samu dan tseren Amurka Tyson Gay da takwaransa na Jamaica tsohon zakaran tseren mita 100 Asafa Powell da laifin amfani da kwayoyin kara kuzari.

Shi kan sa Powell ya tabbatar da sakamakon a wata sanarwa cewa an same shi da laifin amfani da oxilofrine.

Haka ita ma 'yar tseren Jamaican ta mata Sherone Simpson an same ta da laifin amfani da kwayar kara kuzari a gasar kasar ta watan da ya gabata.

Powell mai shekara 30 shi ne dan tseren Jamaica na karshe da ya rike kambun tseren mita 100 kafin Usain Bolt ya karba a 2008.

Kuma har yanzu shi ne na hudu a jerin wadanda suka fi gudu a wannan rukuni na duniya.

Sai dai kuma a wata sanarwa Powell,ya ce shi kam bai taba shan wata kwayar kara kuzari da saninsa ko da niyya ba.

Shi kuwa Tyson Gay dan Amurkan wanda shi ne mutumin da ya fi kowa gudu a 2013 yana jiran sakamako na biyu na binciken da a ke yi akansa.

Kuma tuni ya janye daga shiga gasar tsere ta duniya da za a yi a Moscow,a wata mai zuwa.

Shi ma ya ce ba shi da wata aniya ta aikata abun da ya sabawa ka'ida.

Ya ce, ''na amincewa wani ne kuma ya ci amanata.''

Ya ce, ''na san abin da ya faru, amma yanzu ba zan tattauna batun ba.''

''Fatana dai shi ne na ci gaba da tsere, amma zan amince da duk hukuncin da aka yi min.''