Sharapova ta sauya kociya

maria sharapova
Image caption Sharapova ta raba gari da kociyanta

Ta biyu a jerin gwanayen wasan tennis a duniya mata, Maria Sharapova ta sauya kociyanta.

Sharapova, 'yar Rasha ta nada mutumin da ya taba daukar kofunan manyan gasannin tennis na duniya takwas Jimmy Connors a matsayin sabon kocin nata.

A ranar Alhamis ne, Sharapova wadda Michelle Larcher de Brito ta fitar daga gasar Wimbledon a zagaye na biyu ta bayyana cewa ta rabu da kociyanta Thomas Hogstedt.

'yar wasan mai shekaru 26, ta ce Hogstedt ba zai iya bulaguro ba a nan gaba kadan saboda haka ta yanke shawarar daukar Connors mai shekaru 60.

Da take sanar da rabuwar tata da mai horar da itan, Sharapova ta kara da cewa,''bayan kusan shekaru uku muna tare, ni da Thomas Hogstedt mun yanke shawarar rabuwa.''

Karin bayani