Ameobi ya dawo yi wa Najeriya wasa

shola ameobi
Image caption Shola Ameobi ya ce burinsa shi ne ya taimakawa Najeriya ta je gasar Kofin Duniya

Burin Najeriya na samun dan wasan Newcastle Shola Ameobi ya shigo cikin 'yan wasanta na Super Eagles don taimaka mata a fafutukar da kasar ke yi ta kaiwa ga gasar cin Kofin Duniya da za a yi shekara mai zuwa ya tabbata.

A yanzu dai dan wasan mai shekaru 31 ya samu nasarar kawar da tarnakin da ke kunshe a kwantiraginsa da ya hana shi yi wa Najeriya wasa a gasar kofin kasashen Afrika na 2013.

Tun da farko dai Hukumar Kwallon kafa ta Duniya, Fifa ta baiwa dan wasan wanda ya taba buga wa Ingila wasa a tawagarta ta 'yan kasa da shekara 21, damar shekara daya ya koma yi wa kasarsa ta haihuwa wato Najeriya wasa.

Sau daya dai ya taba buga wa Najeriyar wasa a lokacin da ta yi wasan sada zumunta da Venezuela a Miami ta Amurka a watan Nuwamba na 2012 da Najeriya ta ci 3-1, inda ya ci kwallo ta 3.