Manchester za ta sayi Cesc Fabregas

Cesc Fabregas
Image caption Cesc Fabregas

Kulob din Manchester United ya yi tayin sayen tsohon dan wasan tsakiyar kulob din Barcelona, Cesc Fabregas a kan kudi fam miliyan 25.

Har yanzu dai ana tattaunawa a kan sayen nasa, amma ana ganin farashin da suka taya shi bai kai wanda kungiyar sa ta Barcelona ke nema ba.

Yayin da tsohon dan wasan na Arsenal a karan kansa bai damu da ya bar kulob din nasa ba, kuma an fahimci cewa ya fi son komawa Ingila.