Hazard ya zaku Rooney ya dawo Chelsea

wayne rooney
Image caption Ana danganta Rooney da komawa Chelsea duk da cewa kociyan Man United ya ce ba na sayarwa ba ne

Har yanzu babu tabbas kan ci gaba da zaman Wayne Rooney a Manchester United, wanda tun a watan Mayu ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar.

Yanzu ana rade radin komawar dan wasan na Ingila mai shekaru 27 Chelsea ne, duk da cewa kociyan Man United David Moyes, a baya ya ce ba na sayarwa ba ne.

A kan rade radin ne dan wasan Chelsean Eden Hazard ya ke dokin dawowar Rooneyn.

Hazard ya nuna sha'awarsa ta yin wasa tare da Rooney a Chelsea.

Wani dan wasan da kuma a ke dangantawa da komawa Chelsea shi ne Christian Benteke dan Belgium.

Dan wasan mai shekaru 22, wanda ya ci kwallaye 19 a kakar da ta wuce, ya mikawa kungiyarsa ta Aston Villa takardar bukatar sauya klub.