An warware takaddama kan Mba

Dan wasan Najeriya Sunday Mba
Image caption Dan wasan Najeriya Sunday Mba

Kulob din Warri Wolves da kulob din Enugu Rangers a Najeriya, sun warware takaddamar dake tsakaninsu game da dan wasa Sunday Mba, bayan cimma wata yarjejeniya.

Dan wasan mai shekaru 24 wanda ya zura kwallon da ya baiwa Najeriya nasara a gasar cin kofin Afrika a farkon wannan shekarar, zai ci gaba da zama dan wasan kulob din Warri.

Amma zai buga wa Enugu wasa a zaman dan wasa na aro, har zuwa karshen kakar wasanni a watan Satumba mai zuwa.

Sai dai da wuya Mba ya koma Warri, domin nan da 'yan makonni ne ake sa ran zai koma Turai da buga kwallo.

'Yarjejeniyar dai ta kawo karshen ja-in-jan dake tsakanin kulob din biyu game da dan wasan tsakiyan.

"Mun dauki wannan matakin ne domin kada mu yi masa kafar ungulu, a jaririyar sana'arsa ta taka leda." Inji shugaban kulob din Warri, Amaju Pinnick a lokacin da yake magana da BBC.

A watan Janairun da ya gabata ne Mba ya yi tsammanin zai iya barin Warri Wolves, domin koma wa wani kulob din na cikin gida.

Amma hukumar kwallon kafa ta kasar ta yanke hukunci a watan Maris cewa, kwantiraginsa da Wolves bai kare ba, kuma kulob din Rangers da yake so ya koma sai sun biya kudi domin sayensa.