Maicon ya bar Manchester City

douglas maicon
Image caption Douglas Maicon ya bar Man City bayan ya kasa samun bakin zaren wasansa

Dan wasan Manchester City Maicon ya kammala komawa kungiyar Roma ta Italiya a kan kudin da ba a bayyana ba.

Maicon mai shekaru 31 ya kasa yin wani abin a-zo-a-gani a kakaw wasanni daya da ya yi a Man City bayan da kungiyar ta sayo shi a watan Agusta da ya gabata daga Inter Milan a kan fami miliyan 3.

Dan wasan dan kasar Brazil ya yi ta fama da lafiyarsa da kuma yanayin wasansa a duk tsawon lokacin da ya ke Manchester Cityn, inda ya buga wasanni 13 kawai.

Yanzu dai Maicon ya sake komawa gasar Serie A ke nan wadda ya shafe shekaru shida cikin nasarar daukar kofuna da kungiyar Inter Milan.

Kaurar dan wasan daga Manchester City na daga irin gyaran da sabon kociyan kungiyar Manuel Pellegrini ya ke yi.

Daman Kociyan ya sayar wa Juventus Carlos Tevez, yayin da Kolo Toure da Roque Santa Cruz da kuma Wayne Bridge suka bar klub din bayan kwantiraginsu ya kare.

Inda kuma ya sayo dan wasan tsakiya Fernandinho a kan kusan fam miliyan 30 da Jesus Navas a kan kusan fam miliyan 15, da kuma Alvaro Negredo da ke jiran gwajin lafiyarsa.