Froome ya zama zakaran tseren keke

chris froome
Image caption An haifi Chris Froome a Kenya ne kuma a can ya girma

Dan Birtaniya Chris Froome ya zama zakaran gasar tseren keke ta Faransa ta karo na 100.

Wannan shi ne karo na biyu da dan Birtaniya ya ke zama zakaran gasar a cikin shekaru biyu bayan da Sir Bradley wiggins ya zama na farko a 2012.

A shekarar da ta wuce Froome ne ya zo na biyu a bayan Wiggins wanda shi kuma a bana saboda rauni bai iya shiga domin kare kambin ba.

A don haka Froome mai shekara 28 ya zama na daya a bana a gaban Nairo Quintana na Colombia da Joaiquim Rodriguez na Spain