Barcelona ta nada sabon kociya

gerardo martino
Image caption Kafin nadin Gerardo Martino a Barcelonan ba shi da wata kungiya da ya ke horar wa

Barcelona ta nada tsohon kociyan kungiyar Newell Old Boys ta Argentina Gerardo Martino a matsayin mai horad da 'yan wasanta.

Martino mai shekara 50 zai maye gurbin Tito Vilanova wanda ya ajiye aiki saboda ciwon daji da yake fama da shi a makogwaro.

Martino wanda zai jagoranci kungiyar tsawon shekaru uku zai taho da wasu masu taimaka masa ciki har da Adrian Coria wanda ya horad da Messi lokacin yana matashi a kungiyar ta Newell.

Sai dai kuma sabon kociyan ba zai kama aiki da wuri ba kafin wasan sada zumuntar da Barcelonan za ta yi da Bayern Munich.

Tsohon kocinta Pep Guardiola shi ne ke horar da Bayern din da za su kara ranar Laraba da dare.

Karin bayani