Za a duba lafiyar De Bruyne na Chelsea

Za a duba lafiyar De Bruyne na Chelsea

Dan wasan Chelsea Kevin de Bruyne zai koma London domin duba guiwarsa bayan da ya ji rauni a wasan da suka yi ranar Lahadi a Malaysia.

Image caption Chelsea ta sayi Kevin de Brune a kan fam miliyan 7 daga kungiyar Genk ta Belgium a watan Janairu na 2012

Bayan da ya yi sanadin cin kwallon farko a wasan da suka ci 4-1 dan wasan dan kasar Belgium ya ji rauni yayin da ya ke kokarin cin ta biyu.

Bayan wasan kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ce yana da kwarin guiwa ciwon ba mai tsanani ba ne.

Yanzu dai Bruyne ba zai buga wasan da Chelsea za ta yi da zababbun 'yan wasan Indonesia ba ranar Alhamis.

Amma ana ganin zai dawo cikin tawagar lokacin da za su je Amurka domin wasanninsu na karshe na shirin tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

A ranar Alhamis daya ga Agusta Chelsean za ta yi wasa da Inter Milan a Indianapolis daga jerin wasanni hudu da za ta yi a Amurka.

De Bruyne ya koma Chelsea ne daga kungiyar Genk ta Belgium a kan fam miliyan 7 a watan Janairu na 2012 amma har yanzu bai buga wani wasa na gasa ba.

Sai dai irin yadda ya yi wasa a kungiyar Werder Bremen ta Jamus a matsayin dan wasan aro ya kara fito da shi fili da kuma damar dawowarsa Chelsea.

Yayin da a ke shirin tunkarar sabuwar kakar wasanni.