Fifa ta dage hukuncin Kamaru

mohamed iya
Image caption Zaben shugaban hukumar kwallon Kamaru Mohamed Iya na daga abubuwan da suka jawo wa kasar fushin Fifa

Hukumar kwallon kafa ta Duniya fifa ta dage dakatarwar da ta yi wa kasar Kamaru daga shiga duk wasu wasanni na duniya.

Hukumar ta ce ta dage hukuncin ne bayan da kwamitin gudanar da harkokin wasanni na gaggawa a kasar ya kama aiki.

Abin da ya tabbatar mata da cewa Kamarun ta kama hanyar amfani da ka'idojin Fifa kamar yadda ta bukata tun a baya.

Fifa ta kakabawa kamarun wannan hukunci na dakatarwar ne ranar 4 ga watan yuli bisa katsalandan da gwamnati ke yi a harkokin wasanni.

Musamman mazaben shugabancin hukumar kwallon kafa ta Kamarun.

Yanzu ke nan Kamarun ta samu damar yin wasanta na neman zuwa gasar kofin duniya da Libya ranar 6 ga watan Satumba.

Kamarun ce dai ta ke gaba a rukuninsu da maki daya kuma duk kasar da ta yi nasara ita za ta tsallake zuwa zagayen 'yan goma da za a tankade kasashe biyar da zasu wakilci Afrika a gasar Kofin Duniya.

A halin da a ke ciki kuma Uganda na fuskantar irin hukuncin dakatarwar da Fifa ta yi wa Kamarun.

Ita ma a kan irin dalilan laifukan katsalandan da gwamnati ke yi a harkokin wasanni.

Karin bayani