An haramtawa wasu 'yan Nigeria kwallo

Motar hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya
Image caption Hukumar NFF ta ce za ta buga duka sunayen 'yan wasan da jami'an da kuma hotunansu

An haramta wa wasu 'yan wasan Najeriya buga tamaula har abada, saboda saida wasanni da suka yi.

Haramcin dai ya shafi 'yan wasa da kuma jami'an kulob-kulob hudu da suka kara a wasan raba gardamar da aka yi, wadanda aka samu sakamakon ci 79 ba ko daya da kuma ci 67 da nema.

A wasannin biyu dai kulob din Plato United Feeders sun lallasa Akurba da ci 79-0, yayin da kulob din Police Machine kuma ya doke na Bubayaro da ci 67-0.

Duka kulob-kulob din hudu an haramta musu shiga wasa na tsawon shekaru goma.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta bada shawarar cewa duka jami'an wasannin biyu a haramta musu wasa har abada.

Kulob din Plato united Feeders ta ci kwallaye 72 ne, bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Haka kuma kulob din Police Machine, wanda shi ma sai da aka dawo hutun rabin lokaci, sannan ya zura kwallaye 61 a ragar abokin karawarsa.

Sanarwar da hukumar kwallon kasar ta fitar ta ce "Mun karbi shawarwarin kuma za'a sanar da kulob- kulob din da abin ya shafa da hukmar sa ido a kwallon kafa na jihohin da hukumar kwallon kafa ta Afrika da ta duniya wato FIFA."