Rooney zai yi wasa a Sweden

wayne rooney
Image caption Wayne Rooney ya nuna wa manyan jami'an Man United damuwarsa

Mai horad da 'yan wasan Manchester United David Moyes ya ce yana tsammanin Wayne Rooney zai yi wasan da kungiyar za ta yi da AIK Fotboll ta Sweden ranar 6 ga watan Agusta.

Rooney wanda Moyes ya ce ba za su sayar da shi ba duk da rade radin da a ke yi a kan ci gaba da zamansa a kungiyar, ya koma gida ne daga Thailand a watan Yuli saboda raunin da ya ji a cinyarsa.

Dan wasan mai shekaru 27 ya yi sa'oi 24 ne kawai a rangadin wasanninsu na shirin tunkarar kakar bana amma kuma ana saran zai dawo domin wasan sada zumuntar a Sweden.

Rabon da Rooney ya buga wasa tun lokacin da a ka sako shi daga baya a wasan da Chelsea ta ci su 1-0 ranar 5 ga watan Mayu.

Kuma bai buga wasannin Manchester United din ba guda biyu na karshen kakar wasan da ta gabata.

Karin bayani