Al Ahly da Zamalek sun tashi 1-1

zamalek da al ahly
Image caption An so karawar ta Zamalek da Al Ahly ta zama ba 'yan kallo amma a ka kyale 'yan kallo kadan

Kungiyoyin Al Ahly da Zamalek na Masar masu hamayya da juna sun tashi kunnen doki 1-1 a wasansu na gasar Kofin Zakarun Afrika na rukuni na fark, wato Group A.

Zamalek ce ta fara cin kwallonta minti takwas da fara wasan ta hannun Ahmed Gaafar.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma sai Al Ahly ta samu bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida wanda Mohammed Abo Trika ya ci a minti na 54.

Abo Trika da a ke dauka daya daga cikin gwanayen kwallon kafa da a ka taba samu a Masar ya dawo kungiyar tasa ne bayan ya je zaman aro a kungiyarBaniyas ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

An yi wasan ne a filin wasa na birnin El Gouna ranar Laraban nan, bayan da a ka sake sa rana a ka kuma sauya wurin wasan daga Masar zuwa El Gouna saboda rikicin da a ke yi a Masar sanadiyyar hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

An tsara yin wasan ne ba tare da 'yan kallo ba amma daga baya jami'an tsaro suka yanke shawarar barin 'yan kallo kadan su shiga.

A karshen makon da ya wuce a daya wasan rukunin na daya Group A Orlando Pirates ta Afrika ta Kudu ta yi canjaras ba ci da AC Leorpards ta Congo Brazzaville.

Yanzu dukkanin kungiyoyin rukunin suna da maki dai dai ke nan.

Karin bayani