Suarez zai tattauna da Arsenal

luis suarez
Image caption A watan Janairu na 2011 Suarez ya koma Liverpool a kan fam miliyan 22.7

Luis Suarez zai tattauna da Arsenal amma kuma kungiyarsa ta Liverpool ba ta da niyyar sayar da shi har sai an saye shi a kan farashin da ta yi masa na fam miliyan 50.

Tayin da Arsenal ta yi a kansa na sama da fam miliyan 40 wanda Liverpool ta yi watsi da shi kai tsaye ya sa dan wasan ya nemi ganawa da Arsenal din da kansa.

Wannan shi ne karo na biyu da Liverpool ta ke kin amince wa da tayin da Arsenal wadda ke kokarin karfafa 'yan wasanta na gaba ta ke yi a kan dan wasan dan Uruguay.

Ita ma Real Madrid wadda Carlo Ancelotti ke horar wa har yanzu tana bukatar dan wasan amma ba ta shedawa Liverpool din ba.

Yayin da klub din ke son ci gaba da zaman dan wasan a cikinsa karin tayin da Arsenal ke yi a kansa ka iya zama wani zakaran-gwajin-dafi a gare su.

Sakamakon irin ce-ce-ku-cen da Suarez din ya yi ta samun kansa a ciki a kungiyar ta Liverpool da kuma hukuncin da a ka yi masa na hana shi buga wasanni goma bayan ya ciji Ivanovic na Chelsea, ya sa ya kuduri aniyar barin klub di.

A kakar wasannin da ta wuce Suarez ya ci wa Liverpool kwallaye 30 a wasanni 44.

Karin bayani