Man United ba ta hakura da Fabregas ba

cesc fabregas
Image caption Barcelona ba ta sa Cesc Fabregas a wurin da ya fi son ya yi wasa wato tsakiya

Har yanzu Manchester United ba ta hakura da neman Fabregas ba tana ci gaba da duba yadda Barcelona za ta sayar mata da shi.

Kociyan United din David Moyes ya tabbatar da hakan inda ya ce har yanzu yana harin dan wasan mai shekaru 26 a matsayin na farko da zai dauka tun da ya kama aiki.

Sau biyu Manchestern na taya tsohon dan wasan na Arsenal ba tare da nasara ba.

Tayi na baya bayan nan shi ne wanda ta a ke ganin ta saye shi fam miliyan 30 da sauran 'yan tsarabe-tsarabe.

Amma kuma Barcelonan da alamu ba ta da niyyar rabuwa da dan wasan dan kasar Spain.

David Moyes ya kuma sanar cewa Robin van Persie ya samu lafiya daga raunin da ya ji a cinya.

Kuma zai yi wasan sada zumuntar da za su yi da kungiyar Cerezo Osaka ranar Juma'a.

Karin bayani