Fifa na son Premier ta daina adawa

Boyce na son Premier ta daina adawa

Image caption Sepp Blatter ya ce yin gasar Kofin Duniyar a Qatar a lokacin sanyin ba zai zama da dadi ba ga jama'a

Mataimakin shugaban Fifa Jim Boyce na son hukumomin gasar Premier su mara baya ga shirin sauya lokacin gasar Kofin Duniya ta 2022 da za a yi a Qatar.

Shugaban Fifa, Sepp Blatter ne ya kaduri aniyar sauya lokacin gasar daga lokacin bazara zuwa na huturu saboda tsananin zafi da za a fuskanta.

Amma kuma hukumomin gasar Premier suka nuna adawa da shirin hakan saboda zai rikita gasar ta Ingila.

Masana harkar lafiya sun nuna irin hadarin da ke tattare da yin wasanni a yanayi na tsananin zafi.

Wanda ya kai maki 40 a ma'aunin celcius da kuma zai iya kaiwa maki 50 ma a watan Yuni lokacin da za a yi gasar.

Amma kuma a lokacin huturun yanayin zaimkasance ne kusan maki 20 a ma'aunin celcius.

Sai dai kuma kasar Qatar din ta ce za a yi wasannin a filin wasanni masu na'urorin sanyaya wuri.

Amma kuma hakan zai magance matsalar zafin ne a filayen wasa kawai.

Shugaban gasar ta Premier Richard Scudamore ya nuna damuwarsa a kan shirin dage gasar da cewa ''ba za ta yuwu ba su daga gasar da watanni shida.''

Ya ce za su ci gaba da yakin ganin hakan ba ta tabbata ba.

Karin bayani