Burtaniya ta ga amfanin Olympics

Olympics 2012
Image caption Olympics 2012

Sama da kashi biyu bisa uku na al'ummar Burtaniya sun ce kudin da aka kashe wajen shirya gasar Olympics ta London 2012, fam miliyan tara, ba a yi asara ba.

A cewarsu, sun ga amfanin gasar, kamar yadda sakamakon wani binciken jin ra'ayin jama'a da wani kamfani mai suna ComRes ya gudanar a madadin BBC ya nuna.

Hakan ya nuna cewa kashi 74 cikin 100 na al'ummar kasar na maraba da sake dawo da gasar kasar.

Sakamakon ya nuna cewa yanzu haka mutane sun kara azama tun bayan wasan na Olympics kuma adadin mutanen da ke motsa jiki ya karu da kashi goma sha daya cikin dari idan aka kwatanta da shekara guda da ta gabata--adadin ya kai kashi 24 cikin 100 na wadanda ke tsakankanin shekaru 18 zuwa 24.

Gagarumar gasar da ta London da ma gasar Olympics ta nakasassu sun lamushe kudin da ya haura abin da aka shirya kashewa sau uku wato fam biliyan biyu da dubu dari hudu.

Binciken da gwamnati ta gudanar na baya-bayan nan ya nuna cewa sakamakon shirya gasar, tattalin arzikin Burtaniya ya karu da fam biliyan tara da miliyan dari tara, al'amarin da ya taimaka wajen bunkasa cinikayya da zuba jari.

Manufar binciken, wanda ComRes ya gudanar shekara guda bayan wasan na 2012, inda ya tambayi manyan mutane 3,218, ita ce fahimtar yadda jama'a ke kallon wasan.

Karin bayani