Owen na ganin gangancin Suarez

luis suarez
Image caption A makon da ya wuce Arsenal ta taya Suarez fam miliyan 40 da daya

Micheal Owen ya ce idan Suarez ya bar Liverpool ya koma Arsenal abin zai zama da mamaki.

A makon da ya gabata Liverpool ta ki tayin da Arsenal ta yi wanda ba ta taba yi ba.

Na sayen dan wasa fam miliyan 41 a kan dan wasan dan shekara 26 dan Uruguay, wanda ya ke son tattaunawa da Arsenal.

Tsohon dan wasan na Liverpool Owen, ya ce komawar Suarez Real Madrid ko Barcelona ita tafi dacewa.

Owen mai shekaru 33 da ya ci wa Ingila kwallaye 40 a wasanni 89, ya ce har yanzu yana kokarin fahimtar abin da ya sa Suarez ke son komawa Arsenal.

A ranar Lahadi Suarez ya bugawa Liverpool wasa bayan an sako shi daga baya.

Liverpool ta yi nasara a wasan 3-0 a Thailand.

Karin bayani