Tottenham ba za ta saurari Madrid ba

gareth bale
Image caption Burin Gareth Bale ne ya yi wa Real Madrid wasa

Tottenham ta ce ba za ta sayar da Gareth Bale ba duk da sha'awar da dan wasan ya nuna ta tattaunawa da Real Madrid.

Shugaban kungiyar ta Tottenham Daniel Levy ya ce za su yi watsi da bukatar Real Madrid idan ta nuna sha'awarta a kan Bale.

Kungiyar ta Spain ta kara nuna sha'awarta a kan dan wasan ko da ike dai har yanzu ba ta gabatar wa da kungiyarsa hakan a rubuce ba.

Amma kuma Tottenham din ba ta nuna sha'awar sayar da shi ko da kuwa kudin ya kai fam miliyan 85 da a ke gani Real din za ta saye shi ba.

Shi dai Gareth Bale a nasa bangaren yana son tafiya Real Madrid domin fatansa ne daman ya yi wa kungiyar wasa.

Sai dai kuma har yanzu yana da sauran shekaru uku a Tottenham.

A cikin mako mai zuwa a ke saran Real Madrid za ta gabatar da bukatar sayen dan wasan da ya ci kwallaye 26 a kakar da ta wuce.

Yanzu dai za a jira a ga ko Bale zai buga wasan sada zumunta da Tottenham za ta yi da Monaco a karshen makon nan.

Amma dai tuni a Spain a ke yada jita-jita cewa sabon kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti na shirin karbar dan wasan.

Musamman ganin yadda kociyan ya sauya wa Ronaldo wuri a wasansu da PSG ranar Asabar ya matsar da shi daga bangaren hagu zuwa abin da ya sa a ke ganin yana tsara yadda zai hada Bale da Ronaldo a wasa.

Karin bayani