Bale ya yi yarinta a Real Madrid- Pleat

gareth bale
Image caption Ba kananan kudi Tottenham za ta gani ta sayar da Gareth Bale ba inji Pleat

Gareth Bale ya yi yarinta matuka ya fita waje, kuma zai yi kuskure idan ya bar Tottenham ya koma Real Madrid a bana, inji tsohon kociyan Tottenham David Pleat.

Tsohon kociyan ya ce, ''ina shakkun idan zai ji dadin yin kaurar yanzu, saboda 'yan wasa da yawa ba su yi nasara ba da suka fita wasu kasashen.''

Pleat ya kara da cewa, ''ko da ike dai 'yan kadan sun yi nasara amma galibinsu ba sa dacewa.''

Ya ce, yana ganin zai fi dacewa idan Gareth Bale ya jinkirta, ya ci gaba da kokari a inda ya ke, sai badi ya tafi idan yana son hakan.

Tsohon kociyan na Tottenham ya ce ya san shugaban kungiyar Daniel Levy ba zai taba yarda su rabu da dan wasan ba a yanzu.

Amma kuma ya ce ba kananan kudi za su gani su bayar da kai ba a kan dan wasan.

Ya ce, ''ina ganin idan suka ga kamar fam miliyan 100 a gabansu shi kansa Daniel Levy zai sallama, hatta su kansu masu goyon bayan klub din za su fahimci muhimmancin abin.''

A watan Mayu na 2007 Gareth Bale dan yankin Wales mai shekaru 24 ya koma Tottenham daga Southampton kuma ya sabunta kwantiraginsa da shekaru hudu a watan Yuni na 2012.

Dan wasan ya yi fice ne a kakar wasannin da ta gabata inda ya ci kwallaye 26.

Karin bayani