Kungiyoyin Saliyo sun kaurace wa wasanni

mohamed kallon
Image caption Magoya bayan Mohamed Kallon sun yi zanga zanga kan hana shi takara

Kungiyoyin gasar kwallon kafa ta Premier ta Saliyo sun kauracewa wasanninsu domin nuna rashin yarda da hana Mohamed kallon tsayawa takara.

Hukumomin kasar ne suka hana Mohamed Kallon tsohon dan wasan kasar kuma dan wasan Inter Milan da AS Monaco tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar.

Sun dauki matakin ne a kan cewa bai cimma wata ka'ida ta takarar ba ta kasancewa a kasar a shekaru akalla biyar da suka gabata.

Goma daga cikin kungiyoyin gasar 14 ne suka rubutawa hukumar gasar ta Premier ta Saliyo cewa daga yanzu sun daina yin wasannin gasar da a ke yi saboda haramtawa 'yan takarar zaben su biyar tsayawa.

Kungiyoyin sun ce babu adalci a hukuncin kuma bai dace ba.

Tsohon kyaftin din na Saliyo bayan ganawarsa da shugaban kasar Ernest Bai Koroma a kan lamarin ya shedawa BBC cewa yana da kwarin guiwa za a warware hukuncin wanda ya ce yana da nasaba da siyasa.

Za a gudanar da zaben ne ranar Asabar bayan dagewa da a ka yi ta yi a baya, karkashin jagorancin kwamitin rikon kwarya da Fifa ta nada don gudanar da harkokin kwallon kafar kasar.

A yadda a ke yanzu dai Isha Johansen ita ce 'yar takarar shugabancin daya tilo da a ke ganin za ta zama mace ta farko shugabar hukumar kwallon kafar ta Saliyo.

Karin bayani