Tottenham da Real Madrid za su yi cinikin Bale

gareth bale
Image caption Gareth Bale shi ma yana son tafiya Real Madrid

Tottenham ta yarda ta tattauna da Real Madrid akan batun sayen Gareth Bale kan dala miliyan 126 yayin da shugabannin kungiyarsa ke kara ganin yana son tafiya.

Kafin yanzu dai shugaban Tottenham din Daniel Levy a duk lokacin da aka yi batun cewa ya ke dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Lamarin dai ya kai ga Real Madrid din ta gargadi dan wasan da masu bashi shawara cewa suna son magana daya idan zai dawo ya dawo yanzu in ba haka ba to su sun bar maganarsa.

Wannan shi ya sa shugaban Tottenham din ya shirya tattaunawa da Real Madrid.

Wannan kuma shi zai sa a yi zaman ganawar shugabannin kungiyoyin biyu Daniel Levy da na Real Madrid Florentino Perez ranar 6 ga watan Agusta a Florida.

Tuni Tottenham ta fara neman 'yan wasan da zasu maye gurbin Bale din su kuma karfafa ta.

Sun hada da Roberto Saldado daga Valencia a kan euro miliyan 28 da Paulinho da Nacer Chadli.

Shi kuma dan bayan Romania Vlad Chiriches ana sa ran zai zo a kan euro milian 8 daga Steaua Bucharest.

Karin bayani