Chelsea ta kara bada tayin Rooney

Image caption Wayne Rooney

Manchester United ta ki amincewa da wani sabon tayi daga Chelsea a kan dan kwallon Ingila, Wayne Rooney.

Chelsea ta bada tayin dan wasan mai shekaru 27 a watan Yuli, amma sai United taki aminkewa, amma kuma yanzu Chelsea din ta kara nuna sha'awar sayen dan wasan.

A ranar Lahadi Chelsea ta kara bada tayin pan miliyon 25 a kan Rooney, da kuma wasu 'yan karin kudi amma United ta kara yin burus.

Kocin United David Moyes ya hakikance ba za su sayarda da Rooney ba.

Sai dai kuma Rooney na cikin damuwa game da rawar da zai taka a kulob din, saboda Robin Van Persie ne babban dan kwallon gaba na kungiyar.

Karin bayani