Gareth Bale ya yi rashin nasara

gareth bale
Image caption Gareth Bale mai shekaru 24 ya ci wa Tottenham kwallaye 26 a kakar da ta wuce

Dan wasan Tottenham Gareth Bale ya kasa shiga jerin gwanayen 'yan wasan Uefa uku.

A cikin ukun za a zabi gwarzon dan wasan Turai na hukumar ta kwallon kafa da zai samu lamba.

Christiano Ronaldo da Lionel Messi da kuma Franck Ribery ne suka zama uku daga cikin goman da aka zaba.

Gareth Bale shi ne na takwas bayan zagaye na biyu na zaben da wasu 'yan jarida daga kasashen Turai suke yi.

Za a zabi na daya ne bayan wani zagayen zaben ranar 29 ga watan Agusta.

Robin van Persie da ya taimaka wa Manchester United ta kwato kofin Premier da kwallaye 26 shi ne na goma.

Andres Iniesta na Barcelona shi ne na daya a shekarar da ta wuce.

Karin bayani