Bayern ta rufe kofa: Rummenigge

pep guardiola
Image caption A makon da ya wuce Pep Guardiola ma ya ce yana ganin sun kammala sayen 'yan wasa

Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce da wuya su sake sayen wani dan wasa a bazaran nan.

Ya ce sun gamsu da tarin wadanda suke da su yanzu,da suka saya su Jan Kirchhoff da Mario Gotze da Thiago Alcantra.

A game da maganar Luiz Suarez na Chelsea Rummenigge ya tabbatar da abin da Guardiola ya ce a makon da ya wuce.

Inda ya ce kungiyar ta Bayern ba ta harin sayen dan wasan a yanzu kuma ba za su kara wasu 'yan wasa ba.

Karin bayani