Kociyan Malawi ya hakura da kudi

tom saintfiet
Image caption Tom Saintfiet ya ce burinsa shi ne ya ci Najeriya ya kai Malawi gasar Kofin duniya

Kociyan Malawi Tom Saintfiet ya ajiye bukatarsa ta neman ba shi kudi idan ya yi nasara a kan Najeriya.

Kociyan dan Belgium ya amince ya yi aiki kyauta amma idan suka yi nasara a wasan za a ba shi dala dubu goma.

Malawi tana bayan Najeriya da maki biyu duk wadda ta yi nasara a karawar ta su ita za ta sami shiga zagaye na gaba.

Kociyan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kafafen yada labarai suka yi ta babatu a kan maganar ba shi kudin.

Ya ce shi ba bukatar kudi ba ce ta kawo shi Malawi illa ya ciyar da kasar gaba ya kai ta gasar Kofin Duniya.

Karin bayani