Ivory Coast ta dawo da Drogba

didier drogba
Image caption Didier Drogba na son zuwa gasar cin Kofin Duniya a karo na uku

Ivory Coast ta dawo da Didier Drogba cikin tawagar 'yan wasanta a karon farko tun bayan gasar cin Kofin Afrika.

An gayyaci dan wasan mai shekara 35 ne domin wasan sada zumunta da Mexico a New York ranar 14 ga Agusta.

An ajiye shi ne a karon farko bayan gasar Kofin Afrikan da Najeriya ta ci su kuma ta yi gaba ta dauki kofin a karshe.

Kociyan kasar Sabri Lamouchi bai gayyace shi wasannin neman zuwa gasar Kofin Duniya a watannin Maris da Yuni ba.

Kociyan ya ce sai dan wasan ya inganta wasansa zai dawo da shi.

Ana ganin saboda Drogba ya yi rawar gani a wasan kungiyarsa ta Galatasaray a karshen mako a Arsenal shi yasa kociyan ya sake kiran sa.

Karin bayani