An ci tarar dan wasan Ingila

monty panesar
Image caption Monty Panesar mai shekara 31 bai yi wasan da Ingila ta yi da Australia ba ranar Litinin

'Yan sanda sun ci tarar dan wasan kirket na Ingila Monty Panesar saboda yi wa masu gadin kofar wata mashaya fitsari a jiki bayan ya bugu da barasa.

Panesar wanda ke yi wa kungiyar kirket ta Sussex wasa an same shi da laifin tambele da rashin da'a a wajen mashayar Shoosh ranar Litinin.

Kungiyarsa ta ce tana gudanar da bicike a kan lamarin.

Panesar na cikin tawagar 'yan wasan kirket na Ingila 14 da suka yi nasarar sake rike kofin karawarsu da Australia.

Wasan da aka yi a Old Trafford ranar Litinin.

Sau 164 yana yi wa Ingila wasa, amma baya cikin tawagarta a gasar da za ta yi a Durham da za a fara ranar Juma'a.