Ina nan daram a Barcelona- Fabregas

Image caption Cesc Fabregas

Cesc Fabregas ya ce zai ci gaba da kasancewa tare da Barcelona, abinda ya kawo karshen bukatar Manchester United na sayen dan kwallon.

Barcelona ta ki amincewa da bukatar Manchester United har sau biyu na sayen Fabregas a kan fiye da pan miliyon talatin.

Fabregas yace "Samun nasara a Barcelona shine buri na tun ina karami".

Ya kara da cewar "Ina jin dadin taka leda a Barcelona, kuma banyi magana da wata kungiya ba a cikin shekaru biyu da suka wuce".

Fabregas ya soma kwallonsa ne a Barcelona kafin ya tafi Arsenal sannan a shekara ta 2011 ya kara komawa Nou Camp.

Karin bayani