Arsenal za ta hadu da Fenerbahce

Image caption Arsene Wenger na Arsenal

Arsenal za ta kara da Fenerbahce a wasan kifa daya kwala don neman tsallakewa zuwa wasan rukuni na gasar zakarun Turai.

Gunners za ta kara da tawagar ta kasar Turkiya a ranar 20 ko 21 ga wannan watan, sannan ayi bugu na biyu bayan mako guda a filin Emirates.

Ita kuwa AC Milan za ta kece raini ne da kungiyar PSV ta kasar Holland.

Yadda kungiyoyin za su fafata:

Dinamo Zagreb (Cro) v FK Austria Vienna (Aut)

Ludogorets (Bul) v Basle (Swi)

Plzen (Cze) v Maribor (Slo)

Shakhtyor Karaganda (Kaz) v Celtic

Steaua Bucharest (Rom) v Legia Warsaw (Pol)

Lyon (Fr) v Real Sociedad (Sp)

Schalke 04 (Ger) v FC Metalist Kharkiv (Ukr)

Pacos Ferreira (Por) v Zenit St Petersburg (Rus)

PSV (Ned) v AC Milan (It)

Fenerbahce (Tur) v Arsenal

Karin bayani