Tottenham za ta sayi Capoue

Tottenham ta amince da sayen dan kwallon Faransa, Etienne Capoue wanda ke taka leda a kungiyar Toulouse.

Ana gwada lafiyar dan wasan mai shekaru ashirin da biyar a White Hart Lane.

Rahotanni sun nuna cewar Capoue wanda ya zira kwallaye bakwai a wasannin 33 a kakar wasan data wuce, bisa dukkan alamu za a siyeshi a kan pan miliyon tara.

Capoue zai kasance dan wasa na hudu da Tottenham ta siya a kasuwar musayar 'yan kwallo bayan dan Brazil Paulinho daga Corinthians, sai dan Belgium Nacer Chadli daga FC Twente.

Sai kuma Roberto Soldado daga Valencia wanda ya koma Spurs a kan pan miliyon 26.

Zuwansa White Hart Lane, zai bada damar watakila Scott Parker ya bar kulob din ya koma West Ham ko kuma Queens Park Rangers.

Karin bayani