Bayern da PSG na kokarin kare kofi

Image caption Pep Guradiola da Lauren Blanc

Bayern Munich da Paris St-Germain za su fara kokarin kare kofin da suka lashe a kakar wasan data wuce a ranar Juma'a.

Bayern, wacce ta lashe gasar Jamus wato German Bundesliga a wannan karon, tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola ne zai jagoranci tawagar 'yan kwallon.

Bayern Munich din za ta hadu ne da Borussia Moenchengladbach a wasan farko.

A bangaren Paris St-Germain kuwa Laurent Blanc ne zai jagoranci tawagar 'yan kwallonta, bayan ya maye gurbin Carlo Ancelotti wanda ya koma Real Madrid.

PSG dai za ta garzaya gidan Montpellier ne don su kece raini a wasan farko na kokarin kare kofin data lashe a kakar wasan data wuce.

Karin bayani