Man United ta dauki Community Shield

man u ta ci wigan ta dauki community shield
Image caption Kociyan Wigan da ta fadi daga Premier Owen Coyle ya ce sun yi wasa amma ba su da nasara

Manchester United ta dauki Community Shield bayan ta yi nasara a kan Wigan da ci 2-0.

Robin van Persie ne ya ci kwallayen da suka sa sabon kociyan United ya fara wasansa na gasa na farko da nasara.

Kuma David Moyes din ya fara zamaninsa da nasarar daukar kofi.

A minti shida da fara wasan ya ci kwallon farko sai kuma can a minti na 59 ya kara ta biyu.

Sai dai kwallo ta biyun ta taba kafar James Perch na Wigan ta kauce ta shiga raga.

Ana gasar ne tsakanin kungiyar da ta dauki kofin Premier da kuma wadda ta dauki kofin FA.

Manchester United ta ita ce ta dauki Premier yayin da Wigan ta dauki kofin FA na kakar wasan da ta wuce.

Karin bayani