Tennis: Nadal da Serena sun dauki kofuna

rafeal nadal
Image caption Rafeal Nadal shi ne na hudu a jerin gwanayen tennis na duniya

Rafeal Nadal ya buge Milos Raonic ya dauki kofin Rogers na tennis a Montreal ta Canada.

Nadal dan kasar Spain mai shekaru 27 ya yi nasara ne cikin minti 68 da maki 6-2 6-2.

Tun lokacin da ya warke daga ciwon guiwar da ya yi fama da shi a watan Fabrairu ya yi nasara a wasanni 41 daga cikin 51.

Kafin wannan nasara ya yi galaba a kan na daya a duniya Novak Djokovic.

A wasan kusa da na karshe na gasar ta Montreal.

A mako mai zuwa zai koma matsayi na uku a duniya.

Serena Williams

A bangaren mata Serena Serena Williams ce ta dauki kofin bayan ta murkushe Sorana Cirstea.

Ta daya a duniyar ta casa Cirstea 'yar Romania da maki 6-2 6-0 a cikin sa'a daya da minti biyar.

Wannan shi ne karo na uku da take daukar kofin na gasar ta Canada.

Serena 'yar Amurka wannan shi ne kofi na 54 da take dauka.

Andy Murray

A bangaren 'yan bibbyu kuwa Andy Murray da Colin Fleming 'yan Scotland sun yi rashin nasara a hannun Alexander Peya da Bruno Soares 'yan Austria da ci 6-4 7-6.

Karin bayani