Bolt ya zaku ya je wasan Commonwealth

usain bolt
Image caption Sau shida Usain Bolt yana cin lambar zinariya ta Olympics

Zakaran tseren mita 100 na duniya Usain Bolt ya ce ya zaku ya shiga wasan Commonwealth a karon farko a shekara mai zuwa a Glasgow.

Bolt dan Jamaica ya ci lambar zinariya ta tseren mita 100 a gasar wasanni ta Duniya a Moscow ranar Lahadi.

Bai samu damar shiga gasar ta Commonwealth ba ta 2006 da 2010 saboda rauni da ya yi jiyya.

Kasancewar babu gasar Wasannin Duniya ko ta Olympics a 2014 Bolt yana son kara wata lamabar a jerin wadanda ya samu.

Bolt ya ce yana son ya ci gaba da yin nasara domin a rika ambatonsa da irin su Pele da Maradona da Muhammad Ali.

Karin bayani